1 Afirilu 2026 - 00:26
Source: ABNA24
Isra'ila Ta Ƙoƙarin Maimaita Tarihin Shan Kaye A Karo Na 5 A Labanon

Isra'ila ta koma kudancin Lebanon a wani karon domin maimaita shan kaye karo na biyar. Alamun suna nuna zata maimaita yanayin da ta saba: yaƙin da ya ke ƙoƙarin ƙarewa a cikin fadamar karangiya ga sojojin sahyoniyawa. 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Juan Kabass Viga da Antonio Bita sun yi imani da cewa Isra'ila tana gab da maimaita tarihinta a cikin mamaye kudancin Lebanon; Akwai alamun cewa wannan gwamnatin tana ƙoƙarin sake nutsewa cikin kwatamin cakwalkwalin shan kayi na dogon lokaci. 

Isra'ila Ta Ƙoƙarin Maimaita Tarihin Shan Kaye A Karo Na 5 A Labanon

Wannan lamarin ya zo daidai da ƙara ta'azzarar tsanantawar da sojojin Isra'ila ke yi wa fararen hula na Lebanon, wanda ba wai kawai hakan ya gaza raunana kungiyar Hizbullah ba, har ma ya ƙara karfafa rawar da take takawa a idanun Al'ummar Labanon da duniya ba ki ɗaya. Marubutan biyu sun rubuta a cikin wata Makala a cikin jaridar Al-Pais ta Spain cewa a yau kai hari sojojin Isra'ila na sanyawa a tuna da yanayin Isra'ila na mamayar Kudancin Lebanon tsakanin shekarun 1982 zuwa 2000. A lokacin, yakin ya fara da alkawarin Ƙaƙƙarfan tsaro a kan ƙungiyar 'yantar da Falasdinu, amma bayan shekaru 18 na yaƙin ƙasa, ta ƙare da janyewar gaggawa daga fuskanci Isra'ila; Samfurin da a yanzu ake kokarin maimaita shi tare da shan kaye iri ɗaya a kan Hizbullah - ƙungiyar da aka haife ta daga zuciyar wannan mamayar. 

Isra'ila Ta Ƙoƙarin Maimaita Tarihin Shan Kaye A Karo Na 5 A Labanon

A cewar marubutan, gwamnatin Benjamin Netanyahu da wannan kai harin karo na biyar ya mayar da Isra'ila zuwa matakin farko (bayan 1978, 1982, 2006 da 2024; hare-haren da Isra'ila ke gabatarwa ga ra'ayin jama'ar Isra'ila a kowane lokaci a matsayin ƙoƙari na ƙarshe na tabbatar da Iyakokin arewa na yankunan da aka mamaye, 

Dogon yaƙi Mai Cike Da Ruɗani 

A filin daga, sojojin Isra'ila sun fadada mamayar da suke yi a kudancin Lebanon, inda suka zarce wurare biyar da suka kasance a baya wanda ya saba wa yarjejeniyar tsagaita bude wuta a shekarar 2024. 

Wannan tsananta hare-haren ya kai ga shahadar 'Yan jarida na Lebanon, ma'aikatan kiwon lafiya da manoma, ta yadda ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta sanar da shahadar mutane 1189, ciki har da masu ceto 51 da yara 124. 

Isra'ila Ta Ƙoƙarin Maimaita Tarihin Shan Kaye A Karo Na 5 A Labanon

Marubutan, suna nakalto daga "Maha Yahya" darektan cibiyar Carnegie a Gabas ta Tsakiya yana mai gargaɗin cewa harin zai sa yankin ya zama mai tsanani ayyukan soji da kuma kara wa jama'a wahalhalu kan wanda su ke ciki.

Ya jaddada cewa ci gaba da ayyukan soji yana karfafa dalilan wanzuwar kungiyar Hizbullah har ma da samar da sabbin dakarun gwagwarmaya, musamman yadda aka rufe hanyar diflomasiyya kuma Isra'ila ta yi watsi da shirye-shiryen tattaunawa na Lebanon. 

A halin da ake ciki, ministan tsaron Isra'ila Yasra'il Katz ya yi magana game da shirin mamayewa kusan kashi 10 cikin 100 na yankunan kan iyakar Lebanon - yankin da ya yi daidai da zirin Gaza sau biyu - da nufin korar dakarun Hizbullah. 

A daya bangaren kuma, wani manazarci na Isra'ila Avi Yasakharov ya yi hasashen cewa wannan yakin zai yi tsayi kuma ba tare da tabbatar da kwance damarar kungiyar Hizbullah ba. Duk da ɗaukar su cewa kungiyar Hizbullah ta yi rauni sosai bayan gudanar da ayyuka kamar fashewar hanyoyin sadarwa da kuma kashe jagoranta Sayyid Hasan Nasrallah, ya yi gargaɗin nuna gamsuwar da Isra'ila ta yi kuma ya jaddada cewa har yanzu kungiyar ba ta lalace ba kuma tana da iko da ƙarfin samarwa da sojojin Isra'ila asarar rayuka.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha